‘Yan Bindiga Sun yi wa Dagaci Yankan Rago Sun Kuma Kashe Mutane 8 a Zamfara
Wasu yan bindiga sun kutsa kauyen Tungar Ruwa a jahar Sokoto sun yi wa dagacin garin yankan rago.
Mai magana da yawun yan sandan jahar Mohammed Shehu ya tabbatar da harin amma bai yi cikaken bayani ba.
Wani mazaunin garin shima ya tabbatar da lamarin yana mai cewa ‘yan bindigan sun halaka dagacin ne don yana basu matsala.
Jahar Zamfara – Ƴan bindiga sun yi wa dagacin ƙauye yankan rago sun kuma kashe wasu mutane takwas a Tungar Ruwa a ƙaramar hukumar Anka na jahar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a tsakar daren ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta rawaito. Ƴan bindigan sun shafe awanni yayin harin.
Mai magana da yawun yan sandan jahar Mohammed Shehu ya tabbatar da harin amma bai bada cikakken bayani ba.
Read Also:
Ƙaramar hukumar Anka na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin Zamfara da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga.
Wani majiya daga kauyen ya magantu kan yadda abin ya faru
Mutanen ƙauyen da suka bar gidajensu saboda hare-haren sun yi hijira zuwa hedkwatar hukumar da kuma kananan hukumomin Maru da Talata Mafara.
Wani majiya, Anas Mustapha ya shaidawa Premium Times cewa maharan sun shiga garin a kan babura suka fara hare-harbe a iska a yayin da suka nufi gidan dagacin ƙauyen.
Bayan isarsu gidan, sun fito da shi sannan suka yanka shi a gaban wasu mutanen sa da suka tara a wurin.
Mr Mustapha ya ce
“An kuma tabbatar wasu mutane takwas sun mutu bayan harin. Amma abin da muka fahimta shine dagacin ƙauyen yan bindigan suka zo kashewa. Ka san idan suka lura cewa wani shugaban mutane na basu matsala, kashe shi kawai suke yi nan take.”