Mutane 41 Sun Mutu Sanadiyyar Rashin Tsaro a Sassan Najeriya 
Mutum 41 suka rasa rayukansu sakamakon matsalolin tsaro a sassan Najeriya a makon da ya gabata.
Cikin wadanda aka kai wa hari harda wani jami’in tsaron rundunar farar-kaya na SSS guda da kuma farar-hula 40.
Alkaluman da rahotannin kafafan yaɗa labarai suka tattara bai kunshi wanda babu su a rahotanni ba.
Jaridar Premium Times ta Najeriya ta ce alkaluman na nuna an samu ragin mutanen da ake kashewa da kashi 50 idan aka kwatanta da mutum 123 da aka hallaka a makon baya.
Akasarin kashe-kashen ‘yan bindiga ne suka aitaka a yankunan arewa maso yammaci, sai kuma ‘yan tawayen IPOB da suma suka hallaka wasu.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here