Mutane Sama da 9 Sun Rasa Ransu Sandaiyyar Harin ‘Yan Bindiga a Jahar Kogi
Sama da mutum 9 aka kashe a daren jiya Talata sannan an jikkata da dama a wani harin bindiga da aka kai yankin Bagana da ke karamar hukumar Omala ta jahar Kogi.
Wani mazaunin yankin wanda ya sha da kyar ya shaida cewa ‘ƴan bindigar sun farwa wani shago da ke tsakiyar gari nan take kuma suka kashe mutum hudu.
Read Also:
Sannan ya kara da cewa maharan sun yi ta harbi kan mai uwa dawabi lamarin da ya tilasta wa mutane tserewa.
Ya shaida cewa da idonsa ya kidaya gawwakin mutum 5 daga inda ya buya.
A lokacin tabbatar da harin kakakin ‘yan sanda jahar, DSP William Aya, ya ce wani mutum mai suna Usman Salifu ne ya soma ankarar da ‘yan sanda da misalin 9:30 na dare cewa an kai musu hari.
Ya ce sun kai wadanda aka jikkata asibiti sannan sun yi kokarin tabbatar da ganin cewa tsaro ya dawo yankin a yanzu.