Za mu yi ƙoƙarin Sasanta Tsakaninmu – Iran ga Saudiyya

 

Iran na shirin gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da abokiyar hamayyarta Saudiyya a Iraƙi bayan kafa sabuwar gwamnatin Iran, kamar yadda aka ambato jakadan Iran a Bagadaza yana cewa a ranar Talata

Iran da Saudiyya waɗanda su ne jagororin Shi’a da Sunni a Gabas Ta Tsakiya sun shafe shekaru suna hamayya da juna inda dukkaninsu ke marawa ɓangarori da ke yaƙi a Yemen da Syria da wasu wuraren.

A 2016 suka katse hulɗar diflomasiya tsakaninsu.

A watan Mayu Iran ta fara tabbatar da cewa tana tattaunawa da Saudiyya, tana mai cewa za ta yi ƙoƙarin sun sansanta tsakaninsu.

Tun lokacin ne Iran ta zaɓi mai tsattsauran ra’ayi Ebrahim Raisi, matsayin shugaban ƙasa wanda aka rantsar a ranar 5 ga Agusta.

Sanarwar sabuwar tattaunawar da kamfanin dillacin labarai na ISNA ya sanar na zuwa ne bayan taron ƙasashen yankin da aka gudanar a Badadaza kan tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here