Mutanen da Aka Jikkata Ranar 7 ga Watan Satumba a Abuja, Sun Cancanci Samun Tallafi da Kuma Adalci – DSS

 

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike, kuma za ta riƙa fitar da bayanai lokaci-lokaci, game da batun wasu mutane da aka jikkata sanadin harbin bindiga a kasuwar Garki.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce mutanen da aka jikkata ranar 7 ga watan Satumba a Abuja, sun cancanci samun tallafi da kuma adalci.

DSS ta ce tuni ta kafa kwamiti a cikin gida don yin bincike, kuma jami’anta sun ziyarci mutum biyu da aka jikkata, waɗanda ke kwance suna jinya a asibitoci daban-daban.

Ba a dai saba jin hukumar DSS ta fito bainar jama’a, aƙalla tana nuna nadama a kan irin wannan lamari na zafin hannu da aka zargi wani jami’inta da aikatawa a kan wani ɗan ƙasa ba.

Sanarwar ta ce hukumar tana tuntuɓar dangin waɗanda lamarin ya ritsa da su, kuma za ta ci gaba da bibiyar halin da lafiyarsu take ciki.

Tuni da a cewarta, ta yi alƙawarin biyan kuɗin magani har ma ta ajiye wani ɓangare na kuɗin da aka nema, sannan a yayin ziyarar marasa lafiyan da jami’anta suka kai, hukumar ta bayyana aniyar mayar da su zuwa wani asibitinta da ke Abuja, don samun kulawa mafi inganci.

DSS ta ce ko da yake, hakan ba yana nufin amsa laifi ba ne, tun da a cewarta, har yanzu ba a kammala bincike ba, amma dai hukumar ta yi imani waɗanda abin ya faru da su, sun cancanci a tausaya musu, kuma sun cancanci samun adalci da tallafi.

Ta kuma ja hankulan ‘yan ƙasar da cewa DSS ba ta yi wani katsalandan ba, a binciken da ‘yan sanda ke yi, waɗanda ke tsare da jami’an da ake zargi da hannu a lamarin.

Jaridun Najeriya sun ambato wata sanarwa daga ‘yan sandan Abuja, tana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis 7 ga watan Satumba a babbar kasuwar Garki, inda rigima ta kaure tsakanin ‘yan kasuwar da wasu mutane cikinsu har da wani jami’in hukumar DSS, da wani tela mai suna Muhammad Habibu.

Ta ce ‘yan sanda sun garzaya kasuwar saboda hargitsin da ya tashi, bayan samun rahoton cewa mutanen sun kutsa cikin kasuwar inda suka harbi wani tela mai suna Mubarak Mubarak.

“Wannan lamarin ya janyo har wasu matasa da suka fusata, sun yi yunƙurin auka wa jami’an DSS ɗin, amma ‘yan sanda suka shiga tsakani kuma suka kuɓutar da su. Ta ce a yayin hartsigin, an lalata wani ɓangare na ofishin ‘yan sanda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com