Yaduwar Korona: Adadin Mutanen da Suka Kamu da Cutar Ranar Litinin

Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara.

Yayinda wasu jihohi ke sanar da ranakun komawar su makarantu, wasu na tunanin sake kafa dokar kulle.

Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasar Amurka da Ingila ba.

Mutane 1204 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Litinin, 5 ga watan Junairu 2021, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 91,351 a Najeriya.

Daga cikin mutane sama da 90,000 da suka kamu, an sallami 75,699 yayinda 1318 suka rigamu gidan gaskiya.

Wani sabon nau’in cutar Korona da ya samo asali daga Ingila ya shigo Najeriya makonnin bayan nan.

Lagos-654

FCT-200

Plateau-60

Kaduna-54

Kano-40

Rivers-30

Edo-28

Nasarawa-25

Kebbi-19

Bauchi-18

Oyo-13

Akwa Ibom-12

Bayelsa-11

Ogun-11

Delta-9

Abia-8

Benue-5

Imo-3

Borno-2

Sokoto-1

Osun-1

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here