In Har Mutum Baya Son Zautuwa to ya Dauka Babu Gwamnati – Wole Soyinka ga Gwamnatin Buhari
Farfesa Wole Soyinka ya ce baya son yin magana kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Fitaccen marubucin ya ce idan har mutum baya son ya ‘zautu’ ya fi alheri ya dauka babu gwamnatin.
Duk da hakan, Soyinka ya ce ya yi farin cikin ganin yadda aka gyara da gina sabbin layukan dogo da jiragen kasa.
Fitaccen marubucin Najeriya da ya taba lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce idan har mutum bana son ya zautu, ya rika tsamanin kawai babu gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kasar.
Amma ya bayyana layin dogo da jiragen kasa na Lagos zuwa Abeokuta a matsayin abin ban sha’awa da ya dace a yi tun da dadewa.
Read Also:
Soyinka ya yi wannan jawabin ne yayin hirar da aka yi da shi a Kaftin TV wadda wakilin The Punch ta bibiya.
Da ya ke magana a kan sabbin jiragen, fitaccen marubucin ya ce baya son ya yi magana a kan gwamnatin Muhammadu Buhari domin yana dauka ne tamkar babu gwamnatin.
Da aka tambaye shi ko jiragen kasan sun abu ne da zai saka a yaba wa gwamnatin Buhari, ya ce, “Bana son yin magana a kan gwamnatin Muhammadu Buhari. Ina ganin ya fi zama alheri ga kwakwalwa ta baki daya. Ina iya magana kan wasu abubuwa da ke faruwa a Najeria a yanzu amma ina ganin domin kiyaye lafiyar kwakwalwar mutum, ya fi dacewa ya manta akwai gwamnatin Buhari.”
Marubucin ya ce tsawon shekaru titunan Najeriya sun lalace sun zama tarkon mutuwa yayin da kasar ta yi watsi da jiragen kasa.