ALLAH ya yi wa Mutumin da ya Kera Kofar Ka’aba Rasuwa

 

Shekaru arba’in da uku kenan tun bayan da tsohon sarkin Saudia, Khalidi bin Andul Aziz, ya sauya kofar dakin Ka’aba.

Ya bayar da aikin kera sabuwar kofar ne ga kamfanin Injiniyarin na Sheikh Muhammad bin Badr.

Injiniya Muneer Al-Jundi ne ya kera kofar tare da jagorantar gina ta a wancan lokacin.

Injiniya Muneer Al-Jundi, mutumin da ya kera tare da jagorantar gina kofar dakin Ka’aba ya rasu, yadda Daily Trust ta wallafa.

Daily Trust ta rawaito cewa hukumar kula da Masallatan Haramain da ke kasar Saudia ne ta sanar da mutuwar Injiniya Muneer.

Sanarwar ta bayyana cewa Injiniya Muneer ya rasu ne ranar Laraba a birnin Stuttgart na kasar Jamus.

Hukumar Masallatan Haramain ta yi addu’ar Allah ya yi masa gafara da rahama.

Injiniya Muneer ne ya zana fasalin sabuwar kofar dakin Ka’aba da aka kera da ruwan zinare shekara 44 da suka wuce.

Twitter Khalidi bin Abdul Aziz, sarkin Saudi a wancan lokacin, shine ya zabi Injiniya Muneer daga kamfanin Sheik Mahmud bin Badr domin ya jagoranci kera kofar.

Kamfanin Injiniyarin na Sheikh Mahmud bin Badr ya yi suna wajen fitar da taswira da kere-kere da ruwan zinari.

Kofar dakin Ka’aba da Injiniya Muneer ya kera tana da nauyin kilogram 280 Kuma an shafe shekara guda ana aikinta.

A shekarar 1970 Sarki Khalidi ya bawa Injiniya Muneer aikin kera sabuwar kofar bayan wacce aka saka zamanin sarki Abdul Aziz ta tsufa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here