Mutane 50,000 Sun Rasa Mahallinsu a Sudan ta Kudu – MDD
Majalisar ɗinkin duniya ta ce mutum 50,000 sun rasa matsugunansu a Sudan ta Kudu sakamakon sabon rikicin siyasar da aka soma a ƙarshen watan da ya gabata.
Read Also:
Shugabar da ke kula da ayyukan jinƙai na Majalisar a kasar, Anita Kiki Gbeho, ta ce mutane 10,000 sun tsere zuwa Habasha, kuma rikicin na kawo cikas ga ayyukan agaji.
Sudan ta Kudu na fama da zazzafar adawar siyasa tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon jagoran ƴan tawaye Riek Machar, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙasa a yanzu a cikin gwamnatin haɗin gwiwa.
Ana hasashen mutane aƙalla 400,000 ne aka kashe a yaƙin basasa da akayi tsakanin ɓangarorin biyu wanda ya zo ƙarshe bayan yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗaka a 2018.