Daya daga cikin na hannun daman tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Janar Dambazau mai ritaya ya bayyana ficewarsa daga kungiyar Kwankwasiyya zuwa Gandujiyya.

Idris Bello Dambazau ya rike mukamin kwamishinan ayyuka na musamman a Gwamnatin Kwankwaso da Ganduje. Kana kuma yana daya daga cikin mutanan da ake yiwa kallin ‘Yan gaba gaba a Kwankwasiyya.

Dambazau dai na daga cikin mutanan da suka shahara da sukar Gwamna Abdullah Umar Ganduje a cikin ‘Yan Kwankwasiyya da suke da kusanci da Kwankwaso.

Wannan ficewar ta Dambazau daga Kwankwasiyya ya sanya shakku fa wasu da ke ganin da Kwankwaso da Ganduje duk Abu daya ne, wasa kawai suke da hankalin mabiyansu.

Daya daga cikin ‘Yan jam’iyyar PRP mai hamayya a jihar Kano Mukhtar Abba Darki, na da ra’ayin “Kwankwaso da Ganduje suna yaudarar wanda ya gasgata su ne da sunan akwai sabani a tsakaninsu, amma a zahirin abin ba haka yake ba”

The post Na hannun daman Kwankwaso ya fice daga Kwankwasiyya zuwa Gandujiyya appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here