Littafin Nadama: Cutar Sankara A Fayyace

Littafin Wasan kwaikwayo na NADAMA yana dauke da labarun ma su sanya fargaba, tashin hankali, tausayi, farin ciki, da bakin ciki a zukatan masu karatu, tare da nu ni ga mahimmancin hakuri, gaskia da rukon Amana.

NADAMA, littafin wasan kwaikwayo ne da ya kunshi salo na ilimantarwa, fadakarwa, da wayar da kan Al’umma a kan cututtukan mata da yara irin su cutar sankara da yoyon fitsari, tare da alfanun karatun ‘ya mace domin cigaba da inganta rayuwar alumma gaba daya.

Marubuciyyar, Malama Fatima Sanda Usara, tayi amfani da rayuwar Sa’adatu, wacca ta kasance ‘yar gwagwarmaya me nemawa mata hakkin su domin inganta rayuwar su, tare da basu Kwarin gwiwa da magance matsalolin da ka iya addabar su.

A cikin littafin me shafuka 145, marubuciyar ta Kara fayyacewa cikin salo na fikira a kan mahimmancin ruko da gaskia da amana. Ta hanyar haska rayuwar Malam Salman da Mariya, duk da kasancewar su a cikin talauci, hakan be hana su inganta rayuwar saadatu ba, yarinyar da su ka tsinta, suka raine ta har takai munzalin girma da aure kafin gaskiar asalin su waye iyayen ta ya bayyana.

Sannan marubuciyar tayi tsokaci ta hanyar fayyace irin kalubalen da marasa Galihu musamman daga karkara kan iya fuskanta Yayin ziyartar asibitoci ko Wajan ‘yan Sanda domin taimakon su.

Duba da yadda Malam Salman da Mariya suka ki amince wa da ‘Yansanda a lokacin da suka tsinci sa’adatu, da kuma yadda rashin bincike ya Janyo sanadiyyar mutuwar Salman.

Duk da kasancewar Littafin wasan kwaikwayo ne, amma marubuciyar tayi nasarar bayyana sakon da take son isar wa cikin fejina 145. Ta yi amfani da salon rubutu me sanyaya tausayi, fargaba, da Tashin hankali a zuciyar masu karatu.

Littafin NADAMA ya kan iya sanya NADAMA a zuciyar wanda bai karanta shi ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here