Jirgin Yaƙin NAF ya yi Ruwan Bama-Bamai Kan Taron Mayakan ISWAP a Borno
Rahotanni daga jahar Borno sun nuna cewa sojoji sun hallaka mayakan ISWAP da yawan gaske a wani harin sama da kasa.
A cewar wata majiya, jirgin yaƙin NAF ya yi ruwan bama-bamai ta sama kan taron yan ta’addan da ke tsammanin sabon wali na ciki.
A halin yanzun babu adadin yawan yan ta’addan da suka mutu, amma dai rahoto yace da dama sun mutu, wasu sun jikkata.
Borno – Yan ta’adda da dama sun sheka barzahu yayin da jirgin yaƙin sojin sama (NAF) ya saki ruwan bama-bamai kan taron mayakan ISWAP.
Daily Nigerian ta rahoto cewa jirgin yakin ya hallaka wasu tare da jikkata wasu da dama a Sabon Tumbun da Jibularam, ƙaramar hukumar Marte, jahar Borno.
Yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne ranar Jumu’a, daga harin bama-baman jirgin sojoji, yayin da suke tsaka da gudanar da taro tare da sabon shugabansu, Sani Shuwaram.
Read Also:
Yadda lamarin ya faru Wata majiya daga cikin jami’an tsaron sirri, sun shaida wa PRNigeria cewa sojojin sun farmaki wurin taron sabon walin ISWAP, Sani Shuwaram, da manyan kwamndojinsa.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin sun kai hari wurin taron ta sama da ƙasa, bisa haɗin guiwar NAF da kuma sojojin ƙasa.
Jami’in yace:
“An kai samamen ne bayan samun bayanan sirri, bibiya da kuma nazari da rundunar sojin sama suka yi.”
“Yan ta’adda da yawan gaske sun sheka lahira, ciki har da kwamandoji, mayaƙa da kuma yan Hisbah na tsagin ISWAP.”
Suwa aka tabbatar da sun halarci taron?
A wani bincike da sojojin suka yi ta ƙarƙashin kasa, sun tabbatar da cewa daga cikin manyan
kwamandojin yan ta’addan dake wurin taron har da:
“Muhammed Bako, kwamndan mayaƙa na musamman (Rijal Ann), Muhammad Malumma, alkalin kungiya; Goni Mustapha, limamin ƙungiya; Muhammed Ba’ana, kwamandan kirta da sauransu.”