Kungiyar NAFDAC ta Tsunduma Yajin Aiki

 

Kungiyar ma’aikatan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa sun tsunduma yajin aiki.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke kai ruwa rana da kungiyar malaman jami’a ASUU.

Ya zuwa yanzu dai an samu rabuwar kai a kungiyar, ganin wasu yankunan kasar ba su amince a shiga yajin ba.

Kungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya (MHWUN) na hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta shiga yajin aikin, The Cable ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Laraba a hedikwatar hukumar ta NAFDAC da ke Abuja, shugaban kungiyar Auwalu Yusuf Kiyawa, ya ce yajin aikin ya fara ne daga lokacin da yake magana.

Kiyawa ya ce kungiyar ba za ta janye yajin aikin ba har sai an biya alawus din ma’aikata.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa, yankin Legas da kudancin kungiyar ne kawai suka fara yajin aikin.

Majiyar ta ce duk da cewa kungiyar baki daya ta amince a kan batun jin dadin ma’aikata, kungiyar ta Abuja da Arewacin Najeriya ba su amince da yajin aikin ba a matsayin mafita domin suna ganin bai dace ba.

A cewar majiyar:

“A cewar daraktan gudanarwa, ma’aikatan sun ayyana yajin aikin amma kungiyar ta samu rabuwar kai. “Mutanen Legas/kudu ne suke yajin aiki a halin yanzu. Abuja da yankin Arewa ba su shiga yajin aikin ba. Ba a taru a wuri daya ba. Shugaban yana Legas mataimakin shugaban kuma yana Abuja.

Karin bayani na nan tafe…

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here