Ma’aikatan NAFDAC Sun Tsunduma Yajin Aiki
Abuja-Ma’aikatan hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani kan matsalolinsu da aka gaza magancewa.
An ce ma’aikatan karkashin kungiyar manyan ma’aikata na hukumomi da kamfanonin mallakar gwamnati, da ke cikin kungiyar kwadago ta TUC ne suka shiga yajin aikin.
Ma’aikatan NAFDAC sun shiga yajin aiki
Jaridar Punch ta rahoto cewa ma’aikatan sun tsunduma wannan yajin aikin ne saboda gwamnati ta gaza magance matsalolin karin girma da kuma walwalarsu.
Ma’aikatan sun ce shiga yajin aikin ya zama wajibi la’akari da cewa tarurrukan da suka yi da mahukuntan NAFDAC bai haifar da wani d’a mai ido game da bukatunsu ba.
Fusatattun ma’aikatan sun bayyana cewa har yanzu ba a magance koke-kokensu ba, lamarin da ya sa suka tsuduma yajin aikin inji rahoton Channels.
Read Also:
Bukatun da ma’aikatan suka gabatar
A cikin wata sanarwa da Dakta Ejor Michael, sakataren TUC ya rabawa manema labarai game da sanarwar shiga yajin aikin, ya bayyana cewa:
“Wannan matakin ya biyo bayan gazawar hukumar NAFDAC na magance muhimman batutuwan da aka zayyana a cikin wannan sanarwa”
Sanarwar ta zayyana bukatun da suka hada da:
Bitar jarabawar karin girma ta shekarar 2024
Nada daraktoci na hulda da jama’a da aiyuka na musamman
Daukar nauyin horar da ma’aikata a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas
Gyara abubuwan da ke kunshe a jarabawar karin girma
Bayyana makin APER/PER/KPI a kan lokaci
Duba sharuɗɗan cancanta don zana jarawabar karin girma
Ƙirƙirar ofishin nazartar tunani da dabi’u daidai da sanarwar HOS
Biyan duk kuɗaɗen biso, inshorar rai da alawus ɗin zuwa gida
Biyan bashin albashi ga ma’aikata daga 2022, da sauran bukatu.