Jaruma Nafisa Abdullahi ta Musanta Zargin da Malam Lawal Gusau ya yi Ma ta
Mai rajin kare hakkin dan Adam, malam Lawal Gusau ya yi wa jaruma Nafisa Abdullahi fallasa.
Kamar yadda ya fitar a wata takarda, ya zargeta da fasa kwarin miyagun kwayoyi tare da safarar yara.
Sai dai jarumar ta musanta hakan inda ta zargesa da zama mara aikin yi kuma wanda bai bincike kafin ya fara zargi.
Lawal Muhammad Gusau, mai rajin kare hakkin dan Adam mazaunin garin Abuja, ya zargi jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayooyi da safarar yara.
A takardar korafin da Malam :Lawal Gusau ya fitar a ranar 25 ga watan Disamban 2020, ya ce jarumar ta kware a fataucin kwayoyi da fasa kwabrin yara.
Read Also:
A cewar Gusau, Nafisa ta mallaki kamfaninta mai suna Nafs Entertainment One Dream kuma yana da rijista ne a matsayin na nisahadantarwa, kamar yadda Kannywood Exclusive ta wallafa.
Tana kuma amfani da kamfanin wurin shigar da yara marasa gata a cikin fina-finai a bisa binciken da suka yi.
Miyagun kwayoyin da ake zargin jarumar da fataucinsu sun hada da: Benylin, Codeine, Pantazocine da Tramadol.
Har ila yau, Malam Gusau ya zargi jarumar da fakewa da tafiye-tafiye zuwa Turai inda take tunkaho da fim din da take yi.
Amma hakikanin gaskiya shine ba bahaushiya bace, wata kabila ce mai suna Birom da ke Filato.
Ya nuna takaicinsa da yadda ta yi watsi da al’adun Malam bahaushe a kowanne ala’amari nata.
A yayin da Kannywood Exclusive ta tuntubi jarumar a kan abinda za ta iya cewa kan zargin nan, sai tace “Me kuwa zan ce? dama akwai mutane marasa aikin yi haka a duniya? Bani da kamfani mai wannan sunan.”
Jarumar ta ce mahaifinta cikakken dan Kano ne kuma mahaifiyarta ‘yar Jos ce ba Birom ba.
Tushe: Legit