Kamfanin NAHCO ya Hana Jiragen Sama Sauka ko Tashi a Legas

 

Legas – Kamfanin kula da sufurin jiragen sama na Najeriya, NAHCO, ya fada yajin aiki kan rashin karin albashi, ya hana jiragen sama sauka ko tashi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Litinin.

A bidiyon da jaridar TheCable ta gani, fasinjoji masu tarin yawa sun rasa gaba sun kasa baya inda suke yawo da kayansu a filin jirgin saman.

A daya bangaren, Oluwatosin Oladeinde, CEO na Money Africa a wallafar da tayi a shafinta na Twitter, tace:

“An hana jiragen sama sauka ko tashi a filin jirgin sama na Legas. Babu tashi sannan basu saukar jirage a yanzu, fasinjojin da za su yi tafiya sun makale.”

Karin bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here