Hukumar NAHCON ta ƙara Wa’adin Biyan Kuɗin Aikin Hajjin 2025
Hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta ƙara wa’adin biyan kuɗin aikin hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun 2025.
Read Also:
A cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar sashen watsa labarai ta hukumar, Fatima Usara ta fitar, ta ce hukumar ta ɗauki matakin ne sakamakon roƙon da aka yi a madadin maniyyata aikin hajjin da suka kasa biyan ƙudin aikin kafin ƙarewar wa’adin da aka saka da farko na 31 ga watan Janairu.
Shugaban hukumar ta ƙasa ya buƙaci shugabannin hukumomin aikin hajji na jihohi su tabbatar sun aika kuɗaɗen a kan lokaci, inda ya ce hakan na da muhimmanci ganin cewa Saudiyya ta sanya ranar 14 ga watan Fabrairun 2024 a matsayin ranar ƙarshe na sanya hannu kan kwantiragin da aka yi.