Najeriya na da Kashi ɗaya Cikin Huɗu na Masu Fama da Cutar Zazzaɓin Cizon Sauro – Hukumar Lafiya ta Duniya

 

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na masu fama da cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya, a Najeriya suke.

Daraktar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) shiyyar Afirka, Dakta Matshidiso Moeti ta ce yawan al’ummar Najeriya, ya zama ƙalubale ga matakan da ake ɗauka na rage bazuwar zazzaɓin cizon sauro da ake fama da shi a Najeriya.

Ta bayyana hakan ne a Abuja yayin babban taro da wani babban jami’in shirin Amurka na kakkaɓe cutar maleriya a duniya, Dakta David Walton, da babban jami’in Amurka kan shirin daƙile cuta mai karya garkuwar jiki a duniya, Dr. John Nkengasong da sauransu.

Dakta Moeti ta ce “Nahiyar Afirka na da kaso mafi yawa na masu fama da zazzabin cizon sauro a duniya, wanda ya kai kusan kashi 95 cikin 100 na masu cutar, kuma shi ne yake da kashi 96 cikin 100 na waɗanda suka mutu sanadin zazzabin cizon sauro a shekarar 2021.

“Yayin da Najeriya ke da kusan kashi 27 cikin 100 na masu cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya, duk da haka ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.

“Yawan masu fama da cutar zazzaɓin cizon sauro sun ragu da kashi 26 cikin 100 tun daga shekara ta 2000, wato daga masu kamuwa da zazzaɓin 413 a cikin duk mutum 1,000 zuwa masu kamuwa 302 a cikin duk mutum 1000 a shekara ta 2021.

Haka zalika, mace-mace sanadin cutar zazzaɓin cizon sauro sun ragu da kashi 55 cikin 100, daga kashi 2.1 a cikin mutum 1000 zuwa kashi 0.9 a cikin mutum 1000.”

Moeti ta jaddada muhimmancin samun cikakkun bayanai don jagorantar matakan riga-kafin cutar maleriya da kawar da ita.

Ta kuma jaddada bukatar samar da muhimman bayanai kan yanayin cutar a kowacce jiha ta Najeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Ta ƙara da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya za ta ci gaba da jajircewa wajen ba da gagarumar gudunmawar haɗin gwiwa tare da gwamnatin Najeriya da cibiyoyin samar da kuɗi da abokan ƙawance a Najeriya don inganta zuba kuɗi a fannonin da za su taimaka wajen rage yawan cutar maleriya da sauran cutuka a ƙasar.

A yayin taron, ministan lafiya da walwalar jama’a na Najeriya, Farfesa Ali Pate, ya yaba wa Amurka da sauran abokan huldarsu wajen zuba kuɗi har dala miliyan 900 a shirye-shiryen yaki da cutar zazzabin cizon sauro da cuta mai karya garkuwar jiki da kuma tarin fuka a Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com