Gwamnatin Najeriya ta Bawa Ma’aikata Hutu Ranar Maulidi
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Talata 19 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW wato Maulidi.
Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwmanati.
Cikin wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar.
Da yawa daga cikin Musulmai a faɗin duniya sun ɗauki ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal na a matsayin ranar da aka haifi annabin a garin Makka da ke ƙasar Saudiyya.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here