Gungun Mutane Sun Kashe Mai Kisan Mutane a Kenya
Wani gungun mutane a Yammacin Kenya ya kashe wani mutum mai kisan mutane da ya amsa laifinsa, wanda ya tsere daga hannun ƴan sanda kwana biyu da suka gabata, a cewar ƴan sanda.
‘Yan ƙauyen sun gano Masten Wanjala mai shekaru 20 a wani gida a garin Bungoma kuma suka yi masa duka har ya mutu, a cewarsu.
Hukumomi sun ƙaddamar da wani gagarumin bincike don gano mai laifin wanda ya amsa laifin kashe yara maza ƙanana fiye da 10 cikin shekara biyar.
Ya kuma amsa laifin ba su miyagun ƙwayoyi kuma a wasu lokutan ma yana shan jininsu.
Rahotanni sun nuna cewa ya koma gidan iyayensa – waɗanda suka tsine masa – kuma daga ƙarshe maƙwabta suka shaƙe shi bayan sun gano yana gidan iyayen nasa, kamar yadda wani shaida ya bayyana wa jaridar Standard ta Kenya.
Ana tunanin cewa iyayensa ne suka ga gawarsa duk da cewa ‘yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here