Corona: Cutar ta Kashe ƙarin Mutane 35 a Najeriya

 

Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce cutar korona ta kashe ƙarin mutum 35 cikin kwana ɗaya.

Cikin rahoton da ta wallafa, hukumar ta ce wasu ƙarin mutum 376 sun harbu da cutar.

Mutanen da suka kamun sun fito ne daga jaha 14 na ƙasar. Su ne:

Legas (215)

Rivers (82)

Ondo (16)

Imo (14)

Plateau (12)

Kaduna (10)

Kwara (9)

Ekiti (4)

Bauchi (3)

Delta (3)

Kano (3)

Sokoto (3)

Nasarawa (1)

Oyo (1)

Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 209,173 ne aka tabbatar sun harbu da cutar a Najeriya. Kazalika ta kashe 2,804, sai kuma 197,084 da aka sallame su bayan sun warke.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here