Najeriya na Cikin Aminci Duk da Halin Matsalar Tsaro da Ake Fuskanta – Minista Lai Mohammed

 

Minista Lai Mohammed ya kara wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa game da halin da ake ciki.

Ya bayyana cewa, Najeriya na cikin aminci duk da halin matsalar tsaro da ake fuskanta.

A cewarsa, ya kamata ‘yan Najeriya su guje wa duk wani mummunan hasashe da ake wa kasar.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kasar na cikin aminci a hannun shugaba Buhari duk da kalubalen tsaro da ta ke fuskanta, The Punch ta ruwaito.

Ya shawarci ‘yan kasa da kada su yarda da mummunan hasashe game da Najeriya saboda ba za su zo ba.

Ministan ya fadi haka ne lokacin da ya karbi bakuncin Oluyin na Iyin-Ekiti, Oba Adeola Adeniyi Ajakaiye da mukarrabansa a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.

“Idan ana magana game da tsaro, ina so in yi amfani da wannan dama in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa duk da kalubalen tsaro da muke fuskanta a yanzu, Najeriya na cikin aminci.

Dole ne mu ki amincewa munanan hasashe game da kasarmu saboda ba za su cika ba.

“Yana da mahimmanci ga shugabanninmu a kowane mataki su bai wa mutane kwarin gwiwa maimakon yin kalamai da ka iya kara kawo tashin hankali,” a nakalto Ministan yana fadi a cikin wata sanarwa a shafin na ma’aikatar

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here