Cin Zarafin Jami’anta: Gwamnatin Najeriya ta yi Barazanar Sake Duba Alakarta da Indonesiya

 

Gwamnatin tarayya ta dauki kwararan matakai kan harin da jami’an shige da fice na Indonesiya suka kaiwa jami’in diflomasiyyar Najeriya.

Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama ya ce an kira jakadan Najeriya a Indonesia don tattaunawa.

Ministan ya kuma ce bayan hakurin da jakadan Indonesiya a Najeriya ya bayar, dole ne a hukunta jami’an hukumar shige da ficen

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake duba alakarta da Indonesiya bayan harin da jami’an shige da fice na kasar suka kaiwa jami’in diflomasiyyar Najeriya.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 10 ga watan Agusta.

Onyeama ya kuma ce an gayyaci jakadan Najeriya a Indonesia don ci gaba da tuntuba da kuma bayar da cikakken bayani kan harin.

Legit.ng ta bayyana cewa takaitaccen bayanin Onyeama ya biyo bayan la’antar da ma’aikatar ta yi a baya game da harin wanda aka nada a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.

Dole ne a dau mataki kan jami’an da abun ya shafa

Tun farko ma’aikatar harkokin waje ta ce jakadan Indonesiya a Najeriya ya nemi afuwa kuma jami’an shige da fice da abin ya shafa suma sun ziyarci ofishin jakadancin Najeriya da ke Indonesia don neman afuwar jami’in diflomasiyyar.

Sai dai Onyeama ya ce gwamnatin tarayya na son gwamnatin Indonesiya ta dauki kwakkwaran mataki.

Ya sake nanata cewa dole ne a sanya wa jami’an da ke da hannu cikin wannan takunkumi.

An kuma sake bayyana matsayin Onyeama a cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin waje Esther Sunsuwa ta sanya wa hannu, kuma aka fitar jim kadan bayan kammala taron manema labaran.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here