Ranar da Za’a Fara Rubuta Jarabawar WAEC

 

Lagos – Hukumar dake shirya jarabawar fita daga sakandire a nahiyar Africa ta yamma (WAEC) ta sanar da ranar 16 ga watan Agusta a matsayin ranar da za’a fara jarabawar bana 2021, kamar yadda punch ta ruwaito.

Shugaban hukumar a Najeriya, Mr. Patrick Areghan, shine ya fitar da wannan sanarwar a Lagos ranar Talata.

Sanarwar tace:

“Duba da jadawalin karshe da aka fitar na kasa-da-kasa, za’a gudanar da jabawar ta bana WASSCE 2021 a faɗin nahiyar Africa ta yamma daga Litinin 16 ga watan Agusta zuwa Jumu’a 8 ga watan Oktoba, 2021.”

“Saboda hakane za’a karkare jarabawar a Najeriya ranar 30 ga watan Satumba. Za’a shafe tsawon mako 7 ana gudanar da jarabawar a Najeriya.”

cikakken bayani zai biyo baya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here