Shugabannin Jam’iyyar PDP Sun yi Magana Kan Tsige Uche Secondus

 

Jam’iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta ce ba za’a tsige Prince Uche Secondus daga kujerarsa ba amma za’a gaggauta gudanar da taron gangami a Oktoba.

Asali an shirya gudanar da taron gangamin ne a Disamba, karshen shekara.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sokoto kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP ne yayi sanarwar ranar Talata bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki suka gudanar a Abuja.

A tsokacin da Tambuwal yayi kan barakar dake cikin jam’iyyar, ya ce mambobi sun yarda a hada kai da juna.

Yace:

“Muna farin cikin sanar da cewa mun tattauna dukkan matsaloli kuma mun yanke shawaran cigaba da aiki matsayin ‘yan uwa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here