Abin da Najeriya ke Buƙata a Wannan Lokaci Shi ne Addu’a ga Shugabanni da Al’umma Baki ɗaya – Sanata Goje
Abuja – Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa yadda yake jagorancin ‘yan Najeriya cikin kwarewa.
Sanata Danjuma Goje ya bayyana hakan ne a Abuja yayin karɓar lambar yabo daga ƙungiyar manema labarai ta majalisar dattawa a ranar Litinin.
Sanata Goje ya nemi a taya Tinubu da addu’a
anata Goje ya ce abin da Najeriya ke buƙata a wannan lokaci shi ne addu’a ga shugabanni da al’umma baki ɗaya don nasarar kasar, inji rahoton Vangaurd.
Read Also:
Ya yi addu’a ga Shugaba Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.
Sanata Goje ya kuma yi addu’a ga ma’aikatan majalisar tarayya da ‘yan jarida da ke watsa dukkanin ayyukansu a kullum don wayar da kan ‘yan Najeriya.
Sanata Goje ya kambama majalisar dattawa ta 10
Goje ya ce wannan lambar yabo da aka ba shi tamkar allura ce ta zaburar da shi a kan kara sadaukar da kai wajen yi wa kasa hidima.
Ya bayyana cewa majalisar dattawa ta 10 tana aiki tare da bangaren zartarwa don samar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya.
Yayin da ya ce majalisar na aiki tukuru don ci gaban kasa tun bayan kafuwarta a watan Yunin 2023, Sanata Goje ya jaddada muhimmancin taya Tinubu da addu’a.