Kisa: Najeriya Na Kokarin Ceto Wanda Kasar Saudiyya ta Yanke wa Hukuncin
Hukumomin Najeriya ta tattauna da na Saudiyya kan batun wani dan Najeriya da ke tsare a kasar shekaru 18.
Kasar Saudiyya ce ta zartarwa da Sulaimon Olufemi hukuncin kisa bayan an same shi da laifin kashe dan sanda.
Yanzu haka za a iya yafewa Sulaiman kadai idan yar jami’in mai shekara 20 da ya kashe ta amince.
Read Also:
Shugaban hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta ce gwamnatin Najeriya tana duba lamarin Sulaimon Olufemi wanda kasar Saudiyya ta yankewa hukuncin kisa bisa zargin kashe jami’in dan sanda.
Shugaban NiDCOM ya bayyana haka a wata tattaunawa da iyalan Olufemi wanda suke rokon hukumomin Saudiyya su sakar musu dansu, The Punch ta ruwaito.
Ta ce NiDCOM tana aiki da hukumomin Najeriya da ke Kasar Saudi Arabia, ta kara da cewa ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, yana tattaunawa da hukumomin Saudiyya dangane da batun.
Kuma shugaban kwamitin harkokin waje, Akande Sadipe ya ce.
Yancin Olufemi yana hannun yar dan sandan da ya kashe kuma shekarar ta biyu lokacin. Idan ta yafe masa yanzu tana da shekara 20 zai shaki iskar yanci.