Gwamnatin Najeriya ta Cire Haraji a Kan Iskar Gas da Man Dizil

 

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cire harajin VAT a kan iskar gas da man dizil da sauran su.

Ministan kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana hakan a lokacin da yake bayyana wasu matakai da gwamnatinsu ta ɗauka domin rage wa ƴan Najeriya raɗaɗi.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikar kuɗi, Mohammed Manga ya fitar, wadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin na farfaɗo da ɓangaren iskar gas da man dizil da karya farashinsu.

Sanarwar ta ce, “Gyara tsarin VAT na 2024 na nufin cire harajin VAT a kan wasu muhimman makamashi kamar iskar gas da man dizil da sauransu. Wannan matakin zai rage farashinsu, ya taimaka wajen samar da makamashi sannan ya sauƙaƙa wa ƴan Najeriya komawa amfani da su.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here