Nan Gaba Kaɗan Najeriya Za ta Fara ƙera Makamai Domin Sauƙaƙe Yaƙi da Matsalolin Tsaro – Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan gaba kaɗan ƙasarsa za ta fara ƙera makamai domin sauƙaƙe yaƙi da matsalolin tsaro da take fama da su.
Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin taron da yake jagoranta na kwana biyu a fadarsa kan ayyukan da gwamnatinsa ke gudanarwa a ma’aikatu daban-daban.
Ya ce tuni aka bai wa ma’aikatar tsaro umarnin ƙirƙiro wata masana’anta domin ƙera makamai a cikin gida da zummar biya wa rundunar sojan ƙasar buƙatunta.
Ya ƙara da cewa samar da masana’antar makaman a Najeriya zai bayar da damar rage dogaro da ƙasar ke yi kan ƙasashen waje.
Za a ƙaddamar da shirin ne a ƙarƙashin sashen masana’antu na rundunar sojan Najeriya mai laƙabin Defence Industries Corporation of Nigeria (DICON), a cewarsa.
Ya zuwa yanzu Najeriya ta yi nasarar ƙera jiragen ruwa na soja da wasu ƙananan tankokin yaƙi waɗanda shugaban ya ƙaddamar a ƙarshen 2020.
A watan Yulin da ya gabata ne kuma ƙasar ta karɓi jiragen yaƙi da ta sayo daga Amurka na A-29 Super Tucano, waɗanda Buhari ya ce “ana amfani da su wajen bayar da horo da kai farmaki da tattara bayanai ga dakarun Najeriya”.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here