Najeriya Zata Samu Damar Fitar da Man Fetur Kasashen Waje – Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya kadamar da karamin matatatan man fetur na Waltersmith da ke jihar Imo.
Shugaban kasar ya ce samar da wannan matatan man fetur din zai bawa Najeriya damar fara fitar daman fetur zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita.
Buhari ya bayyana gamsuwarsa da aikin matatan man fetur din inda ya ce za a cigaba da aikin fadada wasu matatun.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya zata fara fitar da man fetur da sauran ababen da ake samarwa daga danyen man fetur zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita bayan kafa.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da karamin matatar man fetur mai tace gangan 5,000 duk rana na Waltersmith da ke Ibigwe a Jihar Imo kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Buhari ya kuma kaddamar da bude fara aikin fadada matatan man da ake sa ran zai rika tace gangan mai 50,000 a duk rana.
Read Also:
A cewarsa, samar da matatun man na daya daga cikin muhimman bangarori hudu da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai karkashin shirin inganta matatun mai tun a shekarar 2018.
Shugaban kasar ya ce ya yi farin ciki da matatan mai na Waltersmith da ke karamar hukumar Ohaji na jihar Imo da aka kammala bayan shekaru biyu da kaddamar da shirin duk da cewa an dade da bawa kamfanoni lasisin kafa matattun man.
“Bugu da kari, aiki yana sauri a sauran wurare uku da aikin farfado da tsofaffin matatu, sauran wuraren da za a samar da wasu matatun.
“Farfado da matatun zai bamu damar zama daya daga cikin manyan masu fitar kayyakin man fetur bawai iya makwabtan kasashe har a kasuwannin duniya. “Irin wannan matatar ita ce irin ta farko mafi girma a fadin kasar.
“Irin rawar da gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar Nigerian Content Development and Monitoring Board (NCDMB) da kuma matatar Waltersmith, sun taka gagarumar gudunmawa wajen saurin aikin a cewar” a cewar sa.
Buhari ya ce aikin fadada matatar zai taimakawa Najeriya wajen farfado da tattalin arziki a kasar.