Na Tabbata Zan Bar Najeriya Fiye da Yadda na Same ta a 2015 – Shugaba Buhari
Cikin jawabinsa na bankwana a safiyar Asabar, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da ƙalubalaen da gwamnatinsa ta fuskanta, musamman game da garkuwa da ɗalibai da kuma matsalar tsaro.
Sai dai duk da haka shugaban ya nuna farin cikin cewa zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015 – lokacin da ya hau mulki.
Read Also:
“Yayin da nake shirin komawa Daura, Jihar Katsina, ina jin farin cikin cewa mun ɗauki hanyar gyaran Najeriya ta hanyar ɗaukar matakai masu muhimmanci,” a cewarsa.
“Ina da ƙwarin gwiwar zan bar mulki a 2023 yayin da Najeriya ta inganta fiye da yadda na same ta a 2015.”
A gobe Litinin Buhari zai miƙa mulki ga Bola Ahmed Tinubu, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, bayan shekara takwas yana jagoranci.