Najeriya na Ci Gaba da Fuskantar Rashin Tsaro a Sassan Kasar da Dama
Wani rahoton da kamfanin Beacon Consulting, mai nazari kan tsaro a shiyyar Afirka ta yamma ya fitar ya nuna cewa fiye da mutum dubu aka kashe a Najeriya a watan Oktoban 2023 sanadiyyar hare-haren `yan bindiga da mayakan Boko Haram.
Kazalika rahoton ya ce fiye da mutum 500 ne aka sace don karbar kudin fansa.
Rahoton da bayyana cewa lamarin tsaro ya kara tabarbarewar a Najeriya, daga watan Satumban wannan shekarar zuwa watan Oktoban da ya wuce.
Read Also:
Kamfanin Beacon Consulting, a rahoton nasa na watan Oktoban da ya wuce ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale ta fannin tsaro a sassan kasar da dama.
Ya ce ana fama da matsalar harin `yan bindiga da wasu kungiyoyi, ciki hár da kungiyar Boko Haram da ta IPOB, wato masu fafutukar ballewa da nufin kafa kasar Biafra.
Kuma alkaluman da kamfanin ya fitar sun nuna an rasa rayukan jama`a, an kuma sace mutane a hare-haren da aka kai kan al`umma a kananan hukumomi 266 da ke fadin Najeriya.
Alƙaluman sun nuna lamarin ya fi kamari ne a arewacin Najeriya, inda aka kashe mutum 326 a jihar Borno, jihar Zamfara kuma an kashe mutum 262, Yobe kuma mutum 60, sai kuma Binuwai 38. Yayin da mutum 39 suka rasu a jihar Rivers, Anambara 27, Lagos kuma 19.