Najeriya na Fuskantar Matsalolin Tsadar Abinci Sakamakon Yaƙin Ukraine
Najeriya da wasu ƙasashen duniya 44 na fuskantar matsalolin tsadar abinci sakamakon yaƙin Ukraine, a cewar wani binciken kamfanin Boston ko BCG mai nazari kan lamura a duniya.
Read Also:
Kamfanin na BCG da ya fitar da rahotonsa mai taken ‘Yaƙin Ukraine da turmutsitsi ciyar da duniya’, ya yi bayyani dalla-dalla kan tasirin yaƙin Ukraine kai-tsaye ga matsalolin abinci a duniya.
Rahoton ya ce ƙasashen da ke cikin wannan akuba ban da Najeriya da sauran yankunan Afirka akwai Kudancin Asiya da Latin Amurka.
BCG ya kuma ce akwai damuwa matuka musamman ga Najeriya da tattalin arzikinta ke cikin wani yanayi ga kuma tasirin da annobar korona ta yi wajen sake kassara kasar.
An kiyasta cewa mutane biliyan 1.7 daga kasashe masu tasowa za su fuskanci matsananciyar yunwa da karuwa farashin makamashi da basuka a cewar Majalisar Dinkin Duniya.