Gaba Dayan Najeriya a Hannun Arewa ta Tsakiya Take – Bukola Sarki

Najeriya gaba dayanta ta dogara ne da arewa ta tsakiya, cewar Dr Bukola Saraki.

Ya ce matsawar yankin ya bunkasa, Najeriya ta bunkasa, saboda tarin ma’adanan da ke yankin.

Saraki ya fadi hakan ne bayan shugabannin NCPF sun kai masa ziyara har gidansa da ke Abuja.

A ranar Juma’a, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce yankin arewa ta tsakiya za su ciyar da kasar nan gaba.

A cewar Saraki, yankin ne zai kawo mafita ga Najeriya nan gaba, The Nation ta ruwaito. Kamar yadda yace, arewa ta tsakiyar tana da ma’adanai masu tarin yawa, wanda hakan zai kawo kudi Najeriya.

Saraki ya bayyana hakan ne bayan shugabannin kungiyar jama’an arewa ta tsakiya (NCPF) sun kai masa ziyara gidansa da ke Abuja.

A cewarsa, arewa ta tsakiya mallakin Najeriya ce, kuma wajibi ne a dubi yankin idan 2023 tayi.

An zabi tsohon shugaban majalisar dattawa a matsayin jigon NCPF, kuma ya nuna farincikinsa na wannan matsayi da aka bashi.

A cewarsa, babban dalilin kirkirar NCPF shine samar da hadin kan ‘yan arewa gabadayansu, sannan da neman shawarwarin juna idan wani al’amari ya bullo.

A cewarsa, “Babban makasudin samar da kungiyar shine kawo cigaba. Yanzu haka hankalin al’umma kada ya koma kan siyasa. Gabadaya kasar nan sun dogara da arewa ta tsakiya saboda ma’adanan da yankin yake da su.”

Saraki ya ce matsawar arewa ta tsakiya ta bunkasa, to Najeriya gaba dayanta ta bunkasa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here