Jadawalin FIFA: Najeriya ta Koma ta 31

 

Najeriya ta koma ta 31 a jerin kasashe mafi kwarewa a kwallon kafa da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya fitar.

Hakan na zuwa duk da Tawagar ta Super Eagles ta lallasa Sao Tome and Principe da ci 10-0, a wasan share fage na gasar cin kofin Afrika.

Sai dai Super Eagles wadda ta nada sabon koci wato Jose Peseiro ta cigaba da zama ta hudu a Afrika.

Najeriya ta fara wannan shekarar ne a ta 32 ta samu ci gaba bayan da ta dawo na 30 a watan Maris, kafin ta kara sauka zuwa ta 31a jadawalin na FIFA.

Senegal wadda itace ta daya a Afrika ta dawo ta 18 a teburin duniya, daga ta 22 a watan Maris.

Sai dai Brazil ta kara bai wa Belgium rata a matsayin ta daya, yayin da Argentina ta sauko da Faransa daga ta uku.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here