Sojojin Israila ne Suka Kashe Shireen Abu Aqla – MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa sojojin Israila ne suka kashe sanannar yar jaridar gidan talabijin na Aljazeera, Shireen Abu Aqla.

Mai magana da yawun Majalisar ta ce wani bincike mai zaman kansa da suka gudanar kan harbin na 11 ga watan Mayu ne ya tabbatar da hakan.

An kashe Shireen yayin da take kawo rahoto kan ayyukan Israila a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Israila ta mamaye.

Kuma tun a lokacin ne Falasdinawa da gidan jaridar na Aljazeera suke zargin dakarun Israila da harbe ta da gangan.To amma Israila ta ce ya yi wuri a iya zarginsu da aikata kisan.

Duniya ta yi tir da kisan yar jaridar mai shekaru 51, duk da tana sanye da rigar kariya daga harsashi, da kuma hular kwano da ke nuna alamun cewa yar jarida ce.

Da take magana da yan jarida a Geneva, Ravina Shamdasani ta ce Ofishin Kare Hakkin Bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewa ” harsashin da ya kashe Abu Aqla da wanda ya jikkata abokin aikinta Ali Sammoudi ya fito ne daga dakarun Israila”.

”Harsashi biyu aka harbo, inda daya ya jikkata Ali Sammoudi a kafada, yayin da daya ya shiga kan Abu Aqla ya kuma kashe ta nan take”, in ji ta.

Sai dai Israila ta ce tana kan gudanar da nata bincike kan kisan, kuma duk da ta gano cewa harsashin bindigar soja ne ya yi harbin, to amma tana bukatar a bata harsashin da ke hannun Falasdinu don ta kammala binciken.

To amma gwamnatin Falasdinu ta ce ba zata bada harsashin ba don bata amince da Isra’ila ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here