Gwamnatin Najeriya ta Buƙaci ƴan ƙasar Mazauna Lebanon su Fice Daga ƙasar
Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM) ta shawarci ƴan ƙasar mazauna Lebanon su duba yiyuwar ficewa daga ƙasar, kasancewar har yanzu jiragen fasinja na jigala a ƙasar.
Read Also:
Cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, Abdur-Rahman Balogun ya fitar ya ce NIDCOM ta ce ta bayar da shawarar ne sakamakon damauwar da take da shi kan hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kai wa Hezbollah da wasu yankunan Lebanon
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta samu labarin yadda kawo yanzu wasu ƴan ƙasar da ke zaune a kudancin ƙasar, sun fice daga yankin, amma duk da haka hukumar ta shawarce su su ci gaba da kasancewa a wurare masu tsaro.
Haka kuma hukumar ta NIDCOM ta shawarci ƴan ƙasar Mazauna Lebanon da su riƙa tuntuɓar ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar, kan duk wani abu da ya shafi tsaron lafiyarsu.