Shimfida Bututun Iskar Gas: Najeriya da Morocco Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar

 

Kasashen Morocco da Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta bayar da damar shimfida bututun iskar gas daga Najeriya zuwa Morocco.

Aikin na tsawon kilomita 7,000 zai hade da bututun arewacin Afirka da ke tura gas zuwa kasashen Turai wanda ke arewacin Morocco.

Shugaban kamfanin mai na Najeriya Mele Kyari ya shaida wa maharta taron sanya hannun wanda aka yi a birnin Rabat na kasar Morocco cewa aikin zai inganta walwalar jama’a tare da magance matsalar hamada da ake fuskanta a wasu yankunan yammacin Afirka.

A watan da ya gabata ne kasar Algeriya ta daina amfani da bututun da ke bi ta Morocco zuwa Spain, abin da ya janyo wa Moroccon koma-baya ta fuskar man gas da kudin fito da kasar ke karba.

A sanarwar da kamfanin na NNPC ya fitar ya ce aikin zai samar wa kasashen yammcin Afirka kudaden shiga ta hanyar karbar kudin fito na gas din da ke bi ta kasashensu.

Kawo yanzu dai ba a san yaushe aikin zai kammala ba, wanda ake sa ran fitar da gas mai tarin yawa a kowacce rana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here