Gwamnatin Najeriya ta Ware N4b ga Rundunar ‘Yan Sandan Kasar Domin Sayen Man Fetur

 

Gwamnatin Buhari ta samar da makudan kudade ga rundunar ‘yan sanda domin sayen man fetur.

Wannan ne karo na farko da aka ware makudan kudade da suka kai biliyoyi domin sayen man fetur.

Hakazalika, ministan harkokin ‘yan sanda ya magantu kan sabon tsarin albashin ‘yan sanda.

Gwamnatin Najeriya ta amince da ware naira biliyan hudu na man motocin aiki na ‘yan sanda a fadin jahohi 36 na kasar hadi da Abuja, BBC Hausa ta ruwaito.

An ruwaito cewa, ministan ma’aikatar harakokin ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya tabbatar da haka a Abuja a ranar Talata.

Ministan ya ce kudin wanda aka ware a kasafin 2021 shi ne karon farko da aka ware wa ‘yan sanda kudin fetur kaso mai tsoka a kasar.

An kara samar da sabbin ci gaba a hukumar ‘yan sanda

Ya kara da cewa Majalisar zartarwa ta tarayya a kwanakin baya ta amince da Ayyukan Musamman na ‘yan sanda don inganta gaskiya da rikon amana tare da zama karin hanyar samar da kudade don inganta ayyukan ‘yan sanda, in ji Daily Trust.

Da aka tambaye shi lokacin da sabon tsarin albashin jami’an ‘yan sanda wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari zai fito, sai ya ce umurnin Shugaban kasa ga Hukumar Biyada Albashi ta Kasa don samar da sabon tsarin albashi mai inganci zai fito nan ba da jimawa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here