HPV: Najeriya ta ƙaddamar da Rigakafin Cutar Kansar Bakin Mahaifa
Najeriya ta kaddamar da shirin allurar rigakafin cutar Human papillomavirus (HPV) wadda ke haifar da cutar kansar bakin mahaifa kashi na farko.
Hakan na nufin za a sanya allurar a cikin jadawalin rigakafin yau da kullun na ƙasa.
Babban maƙasudin wannan yunƙurin shi ne haɓaka karɓar allurar rigakafin da nufin yaƙar cutar kansar bakin mahaifa wadda za a iya guje ma wa ta hanyar rigakafin.
Cutar kansar bakin mahaifa ita ce ta biyu da ta fi kamari a tsakanin mata a Najeriya, kuma ita ce ta hudu da ta fi kama mata a duniya.
Read Also:
Ministan lafiya na Najeriya, Muhammad Pate, ya bayyana wa BBC halin da ake ciki game da cutar kansar bakin mahaifa a ƙasar.
Ya ce, “Aƙalla mata 12,000 ke fama da ciwon kansar bakin mahaifa [a Najeriya] duk shekara, kusan kashi 90% ne ke rasa rayukansu saboda hakan. Dakile shi [Human papillomavirus] a tsakanin ƴan mata masu tasowa, kafin su kamu da kwayar cutar da ke haifar da kansar shi ya sa muka bullo da rigakafin cutar papillomavirus”.
Yunƙurin tabbatar da wannan rigakafin ya sa an tattaro ƴan sa kai da ma’aikatan lafiya sun ziyarci makarantu a faɗin ƙasar ta yammacin Afirka domin wayar da kan yara mata kan mahimmancin rigakafin.