Nan Ba Da Daɗewa Ba, Najeriya Za Ta Ƙirƙiro Da Cryptocurrency(Tauraron Silalla) Nata-Na-Kanta – Babban Bankin Najeriya
Daga Zaharaddeen Gandu
Biyo bayan dakatar da mu’amala da hada-hadar kuɗi a Najeriya, Babban Bankin Najeriya, CBN, ya bayyana shirye-shirye ga ƙasar, na ƙirkirar kuɗinta na zamani, wato taurarin silalla na kirifto.
Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a ranar talata yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron kwana biyu na Kwamitin Manufofin Kuɗaɗe a birnin tarayya Abuja.
A cewar wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar, Mista Emefiele ya ce “bankin ƙoli ya kafa kwamiti kan hakan”
Lokacin da aka tambaye shi ko an tabbatar da CBN sakamakon faɗuwar darajar kuɗi a makonnin da suka gabata? Mista Emefiele ya ce “CBN ta yi bincike, kuma ta gano cewa akwai wani kaso mai tsoka na ‘yan Najeriya da ke da hannu a harkar cryptocurrency”.
Read Also:
“Kada ku sa ni kuskure, wasu na iya zama halal amma na kuskura na ce yawancinsu ba ‘yan halal ba ne, kuma zan tabbatar da hakan”. in ji shi.
“A ƙarƙashin cryptocurrency da bitcoin, Najeriya ta zo ta biyu kenan? Amma a girman tattalin arzikin duniya, Najeriya ta zo ta 27″.
“Don haka, kuna ganin cewa akwai wasu alaƙa? Kuna tsammanin waɗannan ƙasashe waɗanda tattalin arziƙinsu ya kasance na biyu kuma na 26 zai ba ku damar haɓɓaka kasuwancinku na cryptocurrency zuwa matsayi na biyu? idan abin da ke ciki babban abu ne wanda zai amfanar da kowa? ”. Ya tambaya.
Da yake magana a kan fa’idar kasuwar cryptocurrency, Mista Emefiele ya kawo yadda shugaban kamfanin na Tesla, Elon Musk, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa “zai saka hannun jari game da dala biliyan 1.5 a crypto, kuma farashin ya lillinka”.
“Kuma sai ya sake rubutawa a shafinsa na Tweeter, kuma ya nuna damuwa kan kuɗin”. in ji gwamnan CBN.