Amurka: Nasarar Joe Biden Kan Donald Trump

 

Majalisar dokokin Amurka ta tabbatar da nasarar Joe R Biden Jr a matsayin zababben shugaban kasa bayan nasara kan Donald Trump.

Kidayar kuri’un jihar Vermont ta baiwa Joe Biden adadin kuri’un Electoral College 279 da yake bukata tare da mataimakiyarsa, Kamala Harris.

Majalisar datawar Amurka da na wakilai sun yi watsi da bukatar hana Joe Biden kuri’un Georgia da Pennsylvania.

Bayan haka yan majalisar jam’iyyar Republican sun nuna rashin amincewarsu da kuri’un jihar Arizona, Nevada, da Michigan, amma duka akayi watsi.

A karshe, majalisar ta sanar da cewa Joe Biden na jam’iyyar Democrat ya samu jimmilar kuri’un Electoral College 306, yayinda Donald Trump na jam’iyyar Republican ya samu jimillar kuri’ar 232.

Hakazalika, Kamala Harrisa, mataimakiyar Joe Biden ta jam’iyyar Democrat ta samu kuri’u 306, yayinda Mike Pence mataimakin Donald Trump na jam’iyyar Republican ya samu jimillar kuri’ar 232.

Tabbatar da nasarsa ya biyo bayan zanga-zangar da masoya Trump sukayi a ranar Laraba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here