Anyi Nasarar Kama Abdulrasheed Maina

Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, ya matsa layar zana a yayin da kotu ke nemansa a Najeriya.

Bacewar maina ta sa kotu ta tsare Sanata Ali Ndume a gidan yari saboda shine ya karbi belin Maina bisa wasu sharudai.

Yanzu dai, karya ta kare, jami’an tsaro ma su bincike tare da hadu gwuiwar jami’an yaki da cin hanci sun sake cukume Maina a Nijar.

Jami’an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar.

A cewar majiyar jaridar, an samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami’an tsaron Najeriya da Nijar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here