Gwamnatin Jahar Nasarawa ta Nada Mace ta Farko a Matsayin Babbar Jojin Jahar
Gwamna Abdullahi Sule na jahar Nasarawa ya nada Justice Aisha Bashir babbar jojin jahar,
Mai shari’a Aisha Bashir ita ce ta farko mace da ta zama babbar joji tun kafa jihar a shekarar 1996,
Gwamna Sule ya sanar da nadin ta ranar Talata a Lafia, wajen taron karrama tsohon babban jojin jahar da ya yi ritaya.
Gwamna Abdullahi Sule na jahar Nasarawa ya nada Justice Aisha Bashir a matsayin mukaddashin babbar jojin jihar da zata maye gurbin Justice Suleiman Dikko, wanda ya ajiye aiki bayan ya kai shekaru 65 na ajiye aiki, Leadership ta ruwaito.
Read Also:
Gwamnan, wanda ya sanar da nadin a garin Lafia, ranar Alhamis a wani taron karramawa da aka shiryawa tsohon alkalin alkalan, ya ce hakkin sa ne nada alkalin alkalai duk lokacin da bukatar haka ta taso, kuma bukatar ta taso bayan ritayar Justice Dikko.
Gwamnan ya roki tsohon jojin da ya ci gaba da bawa bangaren shari’a goyon baya, lokacin da ya ke aika sakon fatan alheri ga babban joji mai ritaya.
A nata bangaren, Aisha Bashir, wanda itace mace ta farko ta zama babbar jojin jihar tun da aka kafa ta a 1996, ta taya babban joji mai ritaya bisa nasarar kammala aikin sa ga jihar ta kuma yi masa fatan alheri a sauran rayuwar sa.
Sabuwar babbar jojin ta roki gwamnati da ta kara albashin bangaren shari’a, don taimaka wajen magance matsaloli da dama, ta na tabbatar da cewa zata yi abin da ya dace, ba tare da tsoro ko alfarma ba, kuma bisa doron doka.
Taron karramawar ya samu halartar manyan lauyoyi, alkalan manyan kotuna, na majistire da manyan alkalan makwabtan jihohin Benue da Plateau da sauran manyan baki.