Nasarawa: Mutanen da Akai Garkuwa Dasu a Wani masallaci Sun Samu ‘Yanci
An fito da mutanen da aka yi garkuwa da su a masallaci a Nasarawa.
Wannan mummunan lamarin dai ya auku ne a garin Gwargwada-Sabo – Sai da aka tara kudi har Naira miliyan 8.5 kafin ‘yanuwansu su gansu.
Dazu ne jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa mutane 17 da aka yi garkuwa da su a masallaci a Nasarawa a ranar Talata ta da wuce sun samu ‘yanci. An yi sa’a, masu garkuwa da mutanen sun fito da jama’an da su ka dauke. Hakan na zuwa ne bayan iyalan kowane daga cikinsu sun tara N500, 000 sun biya fansa. Jaridar ta ce jimillar abin da aka tara aka biya miyagun ya tashi a kan Naira miliyan 8.5.
Read Also:
An fito da mutanen da aka tsare ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, 2020. An ajiye su a wani daji da ke hanyar Nicha zuwa Sabo a jihar Nasarawa.
Daga nan kowanensu ya nemi babur, aka kai shi gidansa bayan danginsa da sauran na-kusa da su sun sha wahala wajen tara kudin da za su biya a sake su.
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa: “Da farko masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya N1m domin a saki kowane wanda aka damke.”
“Bayan an shawo kansu, su ka amince kowa ya biya N500, 000.” Haka kuwa aka yi, mutane 17 su ka tattara, su ka hada masu Naira miliyan 8.5, kafin a sake su.
Idan za ku tuna daga cikin wadannan Bayin Allah da aka sace har da wani ma’aikacin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Kaduna, mai suna Yusuf Shugar.