Nasarawa: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci, Sun yi Awon Gaba da Wasu Masallata
Ana tsakiyan Ibada, bata gari cikin al’umma sun yi aika-aika
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa milyan hamsin, amma daga baya sun rage – Har yanzu ba’a samu ceto wadanda aka sace daga hannunsu ba Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari Masallaci kuma sun sace mutane 17 a unguwar Gwargwada-Sabo dake garin Gadabuke a jihar Nasarawa.
Read Also:
An tattaro cewa wadanda aka sace sun hada da wani ma’aikacin jami’ar Ahmadu Bello Zariya, mata 3 a wasu maza 13, a cewar rahoton Daily Trust. Wani mazaunin unguwar mai suna Usman ya ce wannan abu ya faru ne daren Talata yayinda ake Sallan Isha’i. “Yan bindigan na shigowa suka fara harbin kan mai uwa da wabi, yayinda sauran suka shiga cikin Masallacin sukayi awon gaba da su cikin daji,” yace. Limamin Masallacin da yaranshi kadai suka tsira.
Iyalan wadanda aka sace sun samu tattaunawa da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci milyan daya-daya kan kowani mutum.
“Da farko sun bukaci milyan 50, amma da muka cigaba da tattaunawa da su, sai suka ce mu biya milyan kan kowani mutum,” ya kara. Duk yunkurin ji daga bakin kakakin yan sandan jihar Nasarawa, ASP Rahman Nansel, ya ci tura