“Na wa za a Sayi Koda ta?” Itace Tambayar da aka fi yi Mana a Shafinmu – Kenyatta National Hospital
Babbar asibitin gwamnati a Kenya ta ce ana samun karuwar mutanen da ke son sayar da kodarsu a asibitin.
Wani sako da Kenyatta National Hospital ta wallafa a shafinta na Facebook na cewa ”Na wa za a sayi koda ta?” itace tambayar da aka fi yi mana a shafinmu.
Read Also:
Sai dai a cewar asibitin tana shawartar mutane da ke da wannan niyya da su fahimci cewa ana bayar da koda kyauta ne ga masu bukata, kuma asibitin bata sayen kodar.
” Mutane su san cewa an haramta sayar da koda. Ana bada ita ne kyauta ga masu bukata idan mutum ya yi niyya,” a cewar sanarwar.
Ana ta’allaka matsatsain da yasa mutane ke son sayar da kodarsu don samun kudi da matsalar tsadar abinci da man fetur.
Ko a farkon watannan Bankin Duniya ya yi gargadin cewa Gabashin Afrika na daga cikin yankunan da ke fuskantar matsin tattalin arziki saboda yakin Rasha da Ukraine, da kuma annobar corona.