Naziru Sarkin Waƙa: Alkali ya bada belin Mawakin
Hukumar tace fina finai ce ta gurfanar da mawaki Naziru Ahmad bisa zargin sakin wakokin da ba’a tace ba.
Naziru Sarkin Waka ya musanta zargin, sai dai kotu ta sanya sabuwar rana don ci gaba da sauraren karar.
Ana ganin cewa mawakin ya soki gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a cikin wasu wakoki biyu Alkalin wata kotun Majistare ya bada shahararren mawaki Naziru Ahmad (Sarkin Waka), a hannun beli akan mutane biyu zasu tsaya masa da kuma kudi naira miliyan daya.
Hukumar tace fina-finai ce ta kama Naziru bisa zargin sakin wasu wakoki biyu “Gidan Sarauta” da kuma “Sai Hakuri”.
Read Also:
Alkalin kotun, Aminu Gabari ya bada belin mawakin bisa sharadin zai gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa kuma dole daya ya kasance mahaifinsa ko dan uwansa, dayan kuma dole ya kasance Wakilin Gabas, Arewa ko Kudu a Kano, ko kuma daya daga kwamandojin Hisba a kananan hukumomi 44 da ke jihar.
Gabari ya kuma ce dukkan wanda zasu tsaya masa dole sai sun mika “fasfo dinsu na fita kasashen waje”.
Tunda farko, Lauyan masu karar ya ce a ranar 12 ga Satumbar 2019 ne mawakin ya aikata laifin, laifin daya sabawa sashe 112 na dokar hukumar tace fina-finai shekarar 2001.
Barista Wada Ya ce an dawo da shari’ar ne daga wata kotun Majistire dake zamanta a Rijiyar Zaki zuwa inda aka bada belin nasa a Nomansland.
Ya kuma bukaci kotun da saka rana don bashi damar gabatar da hujjoji. Wanda ake karar Naziru Sarkin Waka, bai amsa laifin ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kotun ta bada shi a hannun beli ta kuma sanya ranar daya ga watan Disamba don ci gaba da sauraren karar. Sai dai, an gano cewa a cikin wakokin biyu mawakin ya soki gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.