Kano: Za a ɗauki Sababbin Jami’an KAROTA a Jahar

Hukumar ta KAROTA ta jihar Kano ta ce za ta dauki sababbin ma’aikata guda 700.

Hukumar ta ce za a tura sabbin ma’aikatan zuwa masarautun Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

Har wa yau, hukumar ta gargadi al’umma su guji yin talla a wuraren da ba a halasta yin hakan ba Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma’aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan’agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da ‘yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

A cewarsa, za a tura sabbin jami’an da za a dauka zuwa masarautun Bichi, Rano, Karaye da Gaya a jihar.

Mista Dan’agundi ya ce za a tura jami’an zuwa masarautun ne don tabbatar da bin dokokin tuki.

Shugaban ya kuma yi gargadi kan yin talla a wuraren da aka hana yin tallar inda ya ce duk wanda aka samu yana karya dokar zai fuskanci fushin hukuma.

Ya ce, “Mun saka dokoki masu tsauri don tabbatar da wadanda aka hana yin talla ba su dawo ba don irin wahalhalun da suke janyo wa masu amfani da titi.”

Shugaban ya kuma ce nan gaba KAROTA za ta yi hadin gwiwa da Hukumar Kula da Tituna na Kano, KARMA, don yin gyare-gyaren tituna a jihar.

“Za muyi hadin gwiwa da KARMA don magance matsalar ramuka da ke tituna.

“Akwai wasu wuraren da ke bukatar gyare-gyare a tituna da ke bukatar mu bada gudunmawa wurin aikin.

“Za mu iya bada gudunmawar mu wurin saukaka cinkoso a hanyoyin,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here