NBA za ta Hukunta Lauyoyin da Suka Sace Wayoyin Salula a Wurin Taronta a Legas
Kungiyar lauyoyi ta kasa, NBA, ta ce za ta hukunta wasu lauyoyi da suka sace wayoyin salula da barnata kaya a wurin taronta a Legas.
A ranar Laraba wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna wasu lauyoyi suna ta wawaso da sace kayayyaki a wurin taron a Legas.
Rahotanni sun nuna cewa jinkiri da aka samu wurin rabon jakkuna da wasu kayayyaki wurin taron ne ya harzuka wasu lauyoyin suka hargitsa wuri.
Lagos – Olumide Akpata, shugaban kungiyar lauyoyi, NBA, ya ce duk lauyan da aka samu da laifi wurin lalata rumfunan taro, sace wayoyin salula, da dukkan jami’ai, The Punch ta rahoto.
Akpata ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin babban taron kungiyar na kasa da ake gudanarwa.
Ya kuma yi bayanin dalilin da yasa aka samu jinkiri wurin rabon jakkuna a yayin taron.
Ya ce:
Read Also:
“Babu wanda ya ce ba za mu fuskanci matsaloli a rayuwa ba amma abin da ke da muhimmanci shine yadda za mu warware matsalar cikin gaggawa.
“Yan uwa na lauyoyi, ina muku godiya sosai. Da fatan za mu samu cigaba.”
A wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta a ranar Laraba, an ga lauyoyi suna lalata rumfuna a wurin taron da kwace kayayyaki a daren ranar Talata.
Lauyoyi da suka hallarci babban taron karo na 62 na NBA a ranar Talata sun yi koka kan karancin kayayyaki, inda wasunsu suka ce ba su samu jakkuna ba.
Wasu lauyoyin sun koka kan karancin kayayyaki duk da cewa sun tafi wurin tantancewar ba sau daya ba domin tambaya, hakan, a cewarsu ya fusata su.
Amma, an samu jinkiri wurin rabon kayan duk da yawan mutane da ke jira a kan layi.
Daga bisani wasu lauyoyin sun gaza hakuri kuma suka far wa masu tsaro a wurin, suka fara wawason kaya da lalata abubuwa da sace kayayyakin taron.
A bidiyon, an ga wasu lauyoyi suna lalata rumfunan rajitsa da daukan abubuwan da suke so saboda karancin jakukunan taro.